Dubban mutane na cikin matsala a Najeriya
December 20, 2018Talla
Kungiyar agaji ta Red Cross, ta ce dubban 'yan Najeriya da bala'in ambaliya ya daidaita a sassan kasar daban daban na fuskantar barazanar yunwa da cututtukan da kuma ke bukatar mataki cikin gaggawa.
Mutum dubu 200 ne a takaice ambaliyar ta lalata wa gidaje da gonaki, a cewar Abubakar Kende, shugaban Red Cross din a Najeriya.
Akwai kuma akalla mutum 200 da bala'in ya kashe cikin jihohi 12 a bana, baya ga jihohin Naija da Binuwai da lamarin ya fi tsanani a cikinsu.
A kiyasi inji babban jami'in kungiyar agajin, mutum miliyan biyu ne lamarin ya taba wa rayuwa a Najeriyar, yana mai cewa idan ba matakai aka dauka ba, to fa a fuskanci mai muni a nan gaba.