Kananan yara a Kwango na fuskantar cin zarafi
April 11, 2025Talla
Hukumar ta Unicef ta ce a tsukin watanni biyu kacal, kananan yara kusan dubu goma ne suka sami rahotanin an yi musu fyade da ma sauran nau'ika na cin zarafi.
A cewar mai magana da yawun hukumar James Elder, a kowa ne rabin sa'a ana samun rahoton cin zarafin kananan yara a gabashin jamhuriyar Kwango.
Yanzu haka Unicef na fuskantar wawareren gibi a fannin tallafi da take samu, wanda hakan zai bar dubun yara a cikin wani hali na tsaka mai wuya.
Rikicin na Kwango ko baya ga yin illa ga kananan yara, rahotannin sun tabbatar da mutuwar sama da mutum dubu uku tun bayan barkewarsa.
Karin Bayani: Kabila ya sha alwashin shiga tsakani a rikicin Kwango da M23