Donald Trump na neman wa'adi na uku
April 1, 2025Tun bayan sake zaben sa a matsayin shugaban kasar Amurka, Shugaba Donald Trump ya sha bayyana ra'ayin tsayawa takara karo na uku. Yanzu akwai sabbin alamu da ke nuna cewar maganar da yake yi da gaske ne. A cewar Trump, har yanzu akwai hanyoyi da za a iya bi domin yin wa'adi na uku.
A fadar White House, shugaban Amurka ya shaida wa manema labarai cewa da yawa daga cikin magoya bayansa na son ya ci gaba da zama kan karagar mulki na tsawon shekaru hudu bayan wa'adinsa. Da aka tambaye shi ko zai sake tsayawa takara, Trump ya amsa da cewa:
"Mutane suna neman na tsaya takara, ban sani ba, ban taba duba lamarin ba, suna cewa akwai hanyar da za ku iya bi, amma ni ban sani ba, amma ban duba ba tukuna.
Matsala daya kawai Trump yake da ita; wato tsarin mulkin Amurka. A fili yake, ya hana a zabe shi a karo na uku. Kudirin ayar doka na 22 na tsarin mulki ya ce: "Babu wani mutum da za a zaba a matsayin shugaban kasa fiye da sau biyu a Amurka" Amma ya ce yana son yi wa kasarsa aiki. Al'adar cewa shugabannin Amurka na iya yin wa'adi biyu ne kawai na mulki ta fara ne tun daga uban kasa George Washington. Shi ne Shugaban Amurka na farko daga 1789 zuwa 1797, amma ya bar mulki bisa radin kansa bayan wa'adi biyu saboda yawan shekaru.
Kusan shekaru 150, duk wadanda suka gaje shi sun yi riko da wannan doka. Shugaban kasa daya tilo da ya yi aiki na tsawon wa'adi, shi ne Franklin D. Roosevelt - wa'adinsa na mulki ya kasance daga 1933 zuwa 1945. A lokacin yakin duniya na biyu, saboda yanayin siyasa musamman na kasashen waje, ya karya al'adar da ta gabata, ya yi takara a karo na uku, har ma an zabe shi a karo na hudu a 1944, amma ya mutu bayan 'yan watanni. Jim kaɗan bayan mutuwar Roosevelt, majalisar dokokin Amurka ta yanke shawarar cewa wannan ya kamata ya kasance yanayi na musamman na lokaci ɗaya.
Tun a shekara ta 1947, an gabatar da gyare-gyare ga kudirin doka na 22 na kundin tsarin mulkin kasar, wanda aka yi nufin takaita wa'adin shugabancin kasa zuwa wa'adi biyu. Duk jihohin Amurka sun amince da wannan gyara a shekara ta 1951.
Duk da haka, Donald Trump a halin yanzu da alama yana shirin gwada kofofin da za a iya samu a cikin kundin tsarin mulki da ka iya ba shi damar yin aiki fiye da shekaru takwas. A wani yanayi na yin kwaskwarima ga kudin tsarin mulki
Wakilin jam'iyyar Republican Andy Ogles ya gabatar da daftarin gyare-gyare ga majalisar wakilan Amurka a watan Janairu. Gyare-gyaren za su bai wa shugabannin da ba su yi wa'adi biyu a jere ba, damar tsayawa takara a karo na uku. Daftarin kusan an yi shi ne domin Donald Trump. Shin idan a Amurka aka yi tazarce yaya take kuma ga nahiyar Afirka?