Dole ne a yi bincike kan kisan mutum 20 a Khan Yunis - MDD
August 26, 2025Majalisar Dinkin Duniya ta dage kan cewa dole ne binciken da Isra'ila ta ce tana gudanarwa kan mummunan harin da ya yi ajalin mutane 20 ciki har da 'yan jarida biyar a zirin Gaza ya samar da sahihin sakamako domin doka ta yi aikinta.
A yayin wani taron manema labarai a birnin Geneva, kakakin hukumar kare hakkin bil Adama ta MDD Thameen Al-Kheetan, ya ce ba a taba ganin sakamakon wani bincike da Isra'ila ta ce ta yi a kan wasu munanan al'amura da suka faru a can baya ba, a don haka a wannan karo ba bu wani uziri da za a yi wa Tel-Aviv.
Mista Al-Kheetan ya kuma kara da cewa an kashe akalla 'yan jarida 247 a zirin Gaza tun farkon barkewar rikici a tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas bayan harin ranar bakwai ga watan Oktoba na 2023, lamarin da ya ce ya saba wa dokokin yaki.
A jiya Litinin ne dai sojojin Isra'ilar suka kai tagwayen hare-haren a asibiitin Nasser da ke Khan Yunis a kudancin Gaza, lamarin da ya fusata kasashen duniya ciki har da Amurka da China.