Doland Trump ya dage takunkumin da Amurka ta sanya wa Siriya
May 13, 2025Shugaban Amurka Donald Trump ya dauki matakin da ya ba wa kowa mamaki na janye takunkumin da kasarsa ta kakaba wa Syria, a jajibirin ganawarsa da shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar Ahmad al-Sharaa a Saudiyya. A lokacin da yake karin haske kan wannan matsaya a birnin Ryadh inda yake ziyarar aiki, Trump ya ce zai bai wa Siriya damar tsayawa a kan kafafunta, bayan bukatar gaggawar da Yarima mai jiran gadon Saudiyya Mohammed bin Salman ya mika masa. Dama dai al-Sharaa, da ya hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad a watan Disamba, yana daukar matakin diflomasiyya a kasashen Larabawa da na Turai don daina mayar da kasarsa saniyar ware.
Karin byani: Taron kasa da kasa a Saudiya kan Siriya.
A daya hannun, shugaban Amurka Donald Trump da Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman sun rattaba hannu kan abin da aka bayyana a matsayin "yarjejeniyar huldar tattalin arziki", ba tare da yin cikakken bayani kan yawan kudin da ta kunsa ba. Sai dai, jami'an kasashen biyu sun bayyana cewar takardar fahimtar junar ta shafi fannonin tsaro, makamashi, da ma'adanai da horon 'yan sanda.