Shugaban Madagaska ya soke ministocinsa
August 12, 2021Talla
Yanzu haka dai akwai faragbar kasar ta cigaba da fuskantar matsalar cimaka saboda rashin ruwa a shekara ta biyar a jere, matakin da ya shafi tasirin harkar noma don samun abinci.
Wannan dai na zuwa ne bayan da Shugaban kasar Madagaska Andry Rajoelina ya sallami dukkannin minstocinsa saboda rashin taka rawar gani, kazalika shugaban ya rusa majalisar ministocin mako guda bayan kama mutanen da ake zargi ciki har da sojoji da yunkurin kashe shi.