Dimbin darusan da ke cikin kakar-wasa ta Bundesliga
May 21, 2025Babu kungiya da ta fi ba da mamaki a Bundesliga a bana da ta kai yaya-karama Borussia Dortmund, saboda a tsakiyar kakar wasa ta tashi daga matsayi na 12 zuwa na hudu da ya ba ta tikitin shiga gasar zakarun Turai ta badi. Hasali ma, ta harbi tsuntsaye biyu da dutse daya a makon karshe, inda baya ga nasarar da ta samu a kan Holstein Kiel da ci 3-0 a gida Signal Iduna Park, tauraronta dan asalin Guinea Conakry Serhou Guirassy ya ci kwallo da ya tabbatar da shi a matsayin dan wasa da ya zura wa daukacin kungiyoyin kwallon kafar Jamus akalla kwallo daya a raga a bana, baya ga kasancewarsa wanda ya fi cin kwallaye 13 a gasar zakarun Turai.
Bayern Munich ta sake lashe kambun zakara
A bangarenta, bayan tuntuben shekarar da ta gabata, yaya-babba Bayern Munich ta sake lashe kambun zakara a kwallon kafar Jamus, ba tare da yin babakere a gasar kamar yadda ta saba ba, domin 'yar baya ga dangi Holstein Kiel me ta yi nasarar doke ta. Amma bai hana dan wasanta na gaba kuma kyaftin din Ingila Harry kane, samun kofin zakara a karon farko a cikin tarihinsa ba, baya ga takalmin zinare da ya lashe bayan da ya fi kowa zura kwallaye a raga a kakar wasanni ta bana. A irin wannan yanayi ne tauraron Bayern Munich, Thomas Müller, ya buga wasansa na 503 kuma na karshe na Bundesliga, lamarin da ya faranta masa zuciya.
Müller ya ce: " Ina jin dadin yadda mutane suka so abin da na yi a cikin shekaru 15-16 da suka gabata a Bundesliga. Kwarin gwiwa daga magoya bayanmu da ma kasar baki daya da na samu a cikin 'yan makonnin da suka gabata ya ba ni mamaki. A gare ni, rana ce ta musamman, amma ba ta bakin ciki ba. Ina farin ciki da abin da na yi kuma ina kaunar Bundesliga."
Freiburg da Mainz sun ba wa marada kunya
A wannan karon, kungiyoyin da ba su da wadatar kudi ko fitattun 'yan wasa kamar Freiburg da ke a matsayi na biyar da Mainz a matsayi na shida sun burge, ta hanyar cancantar shiga kasar Europa League da Europa League Conference. Amma kuma sabanin haka, RB Leipzig ta tashi a tutar babu saboda ba ta samu tikitin shiga ko daya daga cikin manyan gasannin Turai ba, lamarin da ke zama farau tun bayan da aka fara damawa da kungiyar a Bundesliga a shekarar 2016. Wannan ne ya sa jaridun Bild da Sportschau suka cancaki mai kula da wasanni a RB Leipzig Jürgen Klopp da yi wa kungiya rikon sakainar kashi duk da dimbin arziki da ta mallaka.
Bayer Leverkusen ta kafa wani tarihi a Bundesliga
Ita kuwa Bayer Leverkusen da ta tashi daga matsayi na farko a saman teburi zuwa na biyu, ta buga wasanni 34 a waje ba tare da ta sha kashi ko daya ba. Sai dai mai horaswarta Xabi Alonso, zai bar kungiyar bayan bajintar da ya nuna, inda zai je Spain a bazara domin ya gaji Carlo Ancelotti a Real Madrid. kuma tsohon dan wasan Bayern Munich Xabi Alonso, ya bayyana yadda yake ji bayan shekaru biyu da rabi a matsayin kocin Bayer Leverkusen:
Alonso ya ce: "Dole ne in yi godiya, saboda dawowa Bundesliga a matsayin koci ya kasance wani babi na rayuwata. Mun yi wasa mai ban sha'awa na karshe kuma mun kafa wannan tarihin, wanda yake da mahimmanci, saboda yana nuna ci-gaban kungiyar da 'yan wasanta. kusanci da na samu da wadannan 'yan wasan ya kasance abu na musamman, ga magoya baya kuma, ya kasance kyakkyawan bankwana. "
Wadanda suka koma karamin lig na Bundesliga
Bochum da Holstein Kiel ne kungiyoyin da suka yi bankwana da Bundesliga tare da komawa matakin karamin lig, yayin da FC Köln da Hamburg suka yi nasarar dawowa cikin dangi na babban lig kwallon kafar Jamus