Deutsche Welle za ta dauki mataki kan Rasha
February 3, 2022Talla
Tashar Deutsche Welle, ta bayyana matakin da hukumomin Rasha suka dauka na rufe ofishinta da ke a birnin Mosko a matsayin tsananin wuce gona da iri.
Da ranar Alhamis ne dai ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta sanar shirin toshe tashoshin tauraron dan Adam da ke watsa shirye-shiryen Deutsche Welle a kasar.
Haka ma gwamnatin Shugaba Putin ta soke lasisin aiki na ma'aikatan DW da ke a birnin Mosko.
Babban daraktan tashar ta DW, Peter Limbourg wanda ya yi wannan martani, ya ce tashar DW na shirin daukar mataki na shari'a a kan Rasha.
Rashar ta afka wa DW ne, bayan matakin da hukumar kula da kafafen watsa labaran Jamus ta dauka na hana watsa shirye-shirye cikin harshen Jamusanci a tashar talabijin ta kasar Rasha wato Russia Today.