Daukewar lantarki ta yi sanadin mutuwa a Spain
April 29, 2025Wasu dattawa mutum uku sun mutu a kasar Spain, bayan sun shaki iskar da ta gurbata da sinadarin carbon monoxide sakamakon amfani da injunan janareta a lokacin da aka samu katsewar wutar lantarki a fadin kasar a jiya Litinin.
'Yansanda sun ce an samu gawarwakin dattawan ne a gidansu da ke Taboadela, wani wajen da ke dauke da kimanin mutane dubu da 500 a arewa maso yammacin kasar.
Jami'in agajin gaggawa ne dai suka gano yawan sinadarin carbon monoxide da ke shake a gidan, abin kuma da ya yi sanadin mutuwar tasu.
Wasu kafofin watsa labarai a Spain din ma dai sun ba da labarin mutuwar wata mata sanadin amfani da wutar kyandir a daren da ya gabata.
Mutane da dama ne dai suka yi amfani da kyandir a Spain da Portugal bayan katsewar wutar lantarki na kwana guda, al'amarin da aka jima ba a ga irin sa ba tsawon shekaru a kasashen.