Darasin Rayuwa: Rashin ilimin bokon mata
March 25, 2022Talla
To amma a gefe guda, matan da tun da farkon rayuwarsu iyayensu suka cire su daga makaranta suka aurar da su duk cewa yanzu girma ya fara kamasu,na cizon yatsa kan rashin yin karatun bokon. Ga dai labarin wata matar: ''An yi min auren wuri tun farkon rayuwata. Sanya wasu daga cikin kawayena da muka yi wasan kasa da su a makarantar boko ne ya dasa min muradin yin karatun na zamani tun a farkon rayuwata. Amma sai mahaifina ya nuna cewa shi bai amince mace ta yi karatun boko ba. A sakamakon haka, ina ji ina gani, karatun bokon ya zama “haramiyata”. Haka nan na ci gaba da zama a gida, da lokaci ya yi, mahaifina ya ga na fara tasawa sai ya nemo min miji ya aurar da ni.