Talla
Yanzu haka dai akwai matasa da ake tsare da su a gidajen kurkuku saboda haddasa fitina da tashin hankali a lokutan zabe. Dalili ke'nan da a wannan karon kungiyoyi masu zaman kansu da shugabannin a Legas ke wayar da kawunan matasa a game da batun samar da zaman lafiya a lokacin zabe.