Salon rayuwa
Dandalin Matasa: 27.02.2025
February 27, 2025Talla
Watan Azumin Ramadan, lokaci ne mai falala da daukacin Musulmi ke himmatuwa wajen ibada tare da kara tsarkake zukatansu domin samun kusanci ga ubangiji. Hakazalika a cikin watan Azumin Ramadan a kan jingine duk wasu ayyukan marar kyau da suka yi hannun riga da addini, sannan matasa kan yi amfani da wayoyi hannu domin debe wa kansu kewa ta hanyar bibiyar shafukan sada zumunta dabam-dabam. Sai dai hakan na tattare da hadura da ka iya shafar ibada. Da kasa za a iya sauraron wannan shirin.