Salon rayuwaNajeriya
Dandalin Matasa: 13.02.2024
February 13, 2025Talla
Sana'ar dillanci daya ce daga cikin sana'o'in Hausawa wadda aka shafe lokaci mai tsawo suna gudanar da ita, kuma abun burgewar shi ne sana'a ce da maza kan yi kuma mata ma na yin ta. A shekarun baya dattijai ne ke gudanar da sana'ar to amma yanzu a ‘yan shekarun baya-bayan nan matasa sun rungumi sana'ar. To amma fa har yanzu da sauran rina a kaba kan yadda wasu matasan sun kasa fahimtar tsarin na dillancin gidaje. Daga kasa za a iya sauraron sauti.