Daga darajar gidajen shan magani a Nijar
August 28, 2025Wannan mataki dai, zai matso da asibitocin da za a samu kwararrun jami'an kiwon lafiya kusa da al'umma. Hakan zai bayar da gudunmawa sosai, wajen kula da lafiyar mata da yara kanana da doguwar tafiya ke rage musu kuzarin zuwa asibiti domin neman lafiya. Tuni dai matakin da zai shafi kananan hukumomi guda 16 da ke a cikin gundumomi 10 na yankin mai gidajen shan magani 480, ya fara faranta rayukan 'yan kasa.
Alkaluman Hukumar Kididdiga ta kasar dai, sun tabbatar da cewa jihar Damagaram ce ke kan gaba a yawan al'umma a yankunan Nijar din. Haka kuma yankin na fama da nisan tazara tsakanin gidajen shan magani daga wanan zuwa wancan, inda a baya-bayan sakataren fadar gwamnatin jihar Mahamadu Bureima Mossi ya ce akwai ci gaba a bangaren yawan likitoci amma kuma da sauran aiki a gaba. Karamar hukumar Droum na daga cikin kananan hukumomin 16 da suka dace da wanan aiki.
Su ma kungiyoyin fafutuka irin su SOS Civisme mai yaki da cin-zarafin 'ya'ya mata da yara kanana, ta bakin Hajiya Umma Abbani sun yi marhabin da matakin. To amma a cewar Sanussi Halilu da ake kira Dan Kalibu daya daga cikin mazauna birnin na Damagaram, matakin ba mazauna karkara kadai zai dadada ma ba. Wanan mataki dai zai canja alkalumma game da tafiyar aikin kiwon lafiya musaman a cikin karkara nesa da birane, inda haihuwa a gida ke zaman tamkar wani abun ado.