Dalilan murabus na ministan kuɗin Rasha
September 26, 2011Ministan kuɗin Rasha ya yi murabus sa'o'i kalilan bayan da shugaba Dimitri Medvedev ya neme shi da yin haka sakamakon wani saɓanin ra'ayin da ya kunno kai tsakaninsu game da makomar siyasar ƙasar. Minista Alexei Kudrin ya fito fili ya nuna adawa da duk wani mataki na naɗa shugaba mai ci a yanzu a muƙamin firaminista, da zarar tsohon shugaba Vladimir Putin ya lashe zaɓe mai zuwa.
Shi dai firaminista mai ci a yanzu wato Putin ya bayyana cewar zai tsaya takara a zaɓen shugaban ƙasa da zai gudana shekara mai kamawa idan Allah ya kaimu, tare da alƙawarin naɗa shugaba Medvedev mai ci a yanzu a muƙamin firaminista. kafofin watsa labaran Rasha sun ruwaito cewar an yi misayan zafafan kalamai tsakanin shugaba da kuma minista kudrin a lokacin wani taro a inda ya Medvedev ya danganta minista kudrin da wani "shashasha mai yawan magana".
Sai da minista kudrin ya yi shawara da firaminista Putin sannan ya ajiye aikinsa domin bisa ga dokokin Rasha shugaban ƙasa ba shi da hurumin koran ministan kuɗi.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman