Dalilan da ke sa rikicin gabashin Kwango ci gaba da kamari
Rikice-rikiceAfirka
Mouhamadou Awal Balarabe
March 11, 2025
Yunkurin mayakan M23 da ke samun goyon bayan Ruwanda na baya-bayan nan ya kasance wani sabon babi a tarihin rikici a gabashin Kwango. Ma’adanai masu matukar daraja na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa rikicin. DW ta fayyace wasu batutuwa game da rikicin.