Zanga-zangar dalibai
May 7, 2025Hakikan daliban makarantar share fagen shiga jami'ar ta Lycée Amadu Kuran Daga sun kwashe sa'o'I 48 ba tare da sun shiga azuzuwan daukan darasi ba domin nuna fushin su sakamakon fatali da biya masu bukatun kudi da aka saba ba su daga asusun kungiyar cikaro cikaro da iyaye ke yi duk shekara domin gyare gyre da sayen wasu kayayyaki na karatu da suka yi karamci da ake ce a cewar Issa Hassan Mani Chaibou da ke zaman magatakarda na kungiyar daliban makarantar.
Karin Bayani: Zaben majalisar tuntuba ya bar baya da kura a Zinder
Ganin yadda iyaye ke da ruwa da tsaki a tafiyar ilimin yaran wannan makaranta, domin karin bayani na tuntubi Chaibu Illu da ke zaman mataimaki na farko na shugaban kungiyar iyayen yara game da abin da ya sani inda ya nuna cewa bangaren kula da tafiyar da makarantar sun karbi jika 130 na sefa za su shirya wasanni, na biyu 28 ga watan Afrilu sun tambayi jika 170 na sefa don su yi shirye-shiryen wasanninsu ba su samu ba.
Tuni dai kungiyar malaman makaranta da suka hada da SNEN ta bakin Mujitafa alhaji Abdu mai kula da harakokin ilimi a kungiyar suka fara zargin magabatan jiha da yin sakaci a tafiiyar ilimin karatun boko a wanan makaranta ta Lycée Amadu Kuran Daga.
Kawo yanzu dai magabata ba su ce uffan ba game da wannan al'amari sai dai abin jira a gani yadda za a shawo kan wannan takun saka da iyaye ke kai kawo duk da ma daliban na cewar dokar kungiya ce ta ba su damar a tallafa masu idan sun shirya holewa.