Dakarun RSF sun kona matatun fetur da sansanin sojin Sudan
May 8, 2025Hare-haren jirage marasa matuka na dakarun RSF sun kona cibiyoyin adana man fetur da dama na Sudan da ke birnin Kosti na jihar White Nile a kudancin kasar, kamar yadda rundunar sojin kasar ta sanar a wannan Alhamis.
Karin bayani:Mayakan RSF sun kai hari Port Sudan
Haka zalika dakarun RSF wadanda ke biyayya ga Mohamed Hamdan Dagalo da aka fi sani da Hemedti, sun far wa sansanin sojin ruwan kasar na Flamingo da ke arewacin birnin Port Sudan mai tashoshin jiragen ruwa, hari na biyu kenan a wannan mako.
Karin bayani:Burtaniya ta yi watsi da kafa gwamnatin dakarun RSF a Sudan
Tuni dai sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadin cewa zafafar hare-haren RSF na baya-bayan nan na shirin kara munana halin jin-kan da fararen hular Sudan ke tsaka da fuskanta, kamar yadda mai magana da yawunsa Stephane Dujarric ya sanar.