Artabu tsakanin dakarun Jamhuriyar Nijar da tsageru
April 4, 2020Talla
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce an yi kazamin ban wuta tsakanin dakarunta da masu ikirarin jihadi da ke dauke da makamai inda sojojin gwamnati hudu suka rasa rayukansu yayin da aka halaka tsageru fiye da 60. Sanarwar gwamnati ta ce tsageru kan ababen hawa sun kai farmaki a daren Alhamis a gudumar Tillaberi kusa da iyaka da kasar Mali.
Ma'aikatar tsaron kasar ta ce an kwace makamai da ababen hawa da tsageru suka yi amfani da su domin kai wannan hari. A shekarar da ta gabata an halaka sojoji da dama na gwamnatin Jamhuriyar Nijar yayin artabu da tsagerun masu ikirarin jihadi. Kasashe na dama na Sahel da ke yankin yamamcin Afirka na cikin tashe-tashen hankula tsagerun masu kaifin kishin addinin Islama.