Cutar kwalara ta barke a Sudan
May 27, 2025Ma'aikatar Lafiya ta Sudan ta bada rahoton barkewar cutar amai da gudawa, lamarin da ya halaka mutum 172.
Sanarwar ta hukumomin Sudan mai fama da yaki ta kuma ce an samu mutum 2,700 da suka kamu da cutar ta kwalara a cikin mako guda.
Sudan: RSF ta ayyana kafa gwamnatin hadin kan kasa
Kashi 90% na mutanen da ke fama da cutar a Khartoum babban kasar suke kuma suna cikin mawuyacin hali a cewar sanarwar ta Ma'aikatar Lafiya ta Sudan.
Ana fama da rashin ruwan sha da lantarki a birnin na Khartoum sakamakon gwabza yaki tsakanin sojin na Sudan da kuma dakarun kar ta kwana na RSF.
Dakarun RSF sun kona matatun fetur da sansanin sojin Sudan
Yaki tsakanin RSF da sojin na Sudan ya barke ne tun a watan Afrilun 2023, lamarin da ya haddasa asarar dubban rayuka da kuma tserewar miliyoyin mutane.