Cire kariya ga ɗan majalisa a Nijar da ake zargi da aikata ba daidai ba
November 24, 2011A jamhuriyar Nijar wasu ƙungiyoyin farar hula na ƙasar sun yi kira ga gwamnati da majalisar dokokin ƙasar da su gaggauta ɗaukar matakan cirewa ɗan majalisar dokokin nan da ake zargi da aikata almundahna ta sama da biyan ɗaya da rabi wato Alhaji Zaku Jibbo zakai rigar kariyarsa domin baiwa kotu damar tuhumarsa sannan kuma sun bukaci da ɓangarorin biyu da su bayar da haske akan wasu rahotanni da ke rawaito ɓacewar takardar neman cire rigar kariyar da gwamnati ta shigar a gaban majalisar dokokin.
Tun dai bayan da majalisar dokokin ƙasar Nijar ta koma zamanta a farkon watan Oktoba 'yan ƙasarr da dama su ka yi zaton maganar cirewa wannan ɗan majalisar dokoki Zaku Jibbo rigar kariyarsa domin sauraransa a gaban kuliya, sai dai kuma maganar ta ƙi bayyana a cikin jadawalin jerin ayyukan da majalisar za ta gudanar a wanann zama nata. To saidai kuma daga bisani wasu kafofin yaɗa labarai na ƙasar ta Nijar suka ruwaito cewa gwamnati ta shigar da wannan bukata a gaban majalisar, hasali ma wasu mujallu na ƙasar su ka wallafa takardar neman cire rigar kariyar da babban alƙali mai shigar da ƙara da suna gwamnati cewa da PROCUREUR ya rubuta, takardar da rahotannin su ka cewa hukumar zartarwar majalisar dokokin ƙasar ta Nijar ta ce ba ta shigo a hannunta ba. Waannan ce ta sanya wau ƙungiyoyin fararan hula na ƙasar su ka soma yin kira na neman majalissar da gomnatin kasar su fito su baiwa 'yan ƙasa bayanin abun da ke faruwa.
Ita ma dai daga nata ɓangare ƙungiyar MONSADEM ta bakin shugabanta MALM SULE UMARU cewa ta yi ba mamaki 'yan majalisar dokokin ƙasar su ɓoye wannan takarda.
TO amma lokacin da yake mayar da martani kan waɗannan zarge zarge majalisar dokokin Nijar ta bakin daya daga cikin mambobin komitin zartarwar majalisar HONORABLE Mahamman Sani Amadu cewa ta yi wannan takarda ba ta iso hannunta ba.
Yanzu dai 'yan Nijar sun zura ido su ga y adda gwamnati dama majalisar dokokin za ta tunkari wannan magana ta cire rigar kariya ga ɗan majalisa Zaku Jibbo, matakin da 'yan ƙasar da dama ke bayyana shi a matsayin zakaran gwajin aniyar gwamnatin Alhaji Mamman Issoufou kan maganar nuna ba sani ba sabo a cikin shirinta na tsarkake tattalin arzikin ƙasar da tayi wa 'yan Nijar ɗin alƙawari lokacin hawan milkinta.
Mawallafi: Gazali Abdu Tasawa
Edita: Mohammad Nasiru Awal