Cinikin 'yan wasa mafi tsada a Bundesliga
Daga Bundesliga zuwa Premier League, shahararren dan wasa Florian Wirtz ya sauya sheka daga Bayer Leverkusen zuwa FC Liverpool a kan kudi Euro miliyan 150, ya zama dan wasa mafi tsada da aka sayar a Bundesliga.
Omar Marmoush - Ero Miliyan 75
Kasuwa ta bude ga Eintracht Frankfurt! A lokacin bazara ta shekara 2023 dan kasar Masar din da ya ke da kwantirage da abokiyar hamayya VfL Wolfsburg, ya sauya zuwa kungiyar ta Hasee a kyauta. Shekara guda da rabi bayan komawarsa, Frankfurt ta sayar da shi a kan makudan kudi Euro miliyan 75 da yiwuwar samun karain garabasa ta Euro miliyan biyar ga kungiyar kwallon kafa ta Manchester City.
Kevin De Bruyne - 76 Millionen Euro
Bayan an amince da sayar da shi a kan kudi Euro miliyan 76, shararren dan wasan na VFL Wolfsburg ya amince da sanya hannu a kan kwantiragi da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City a bazarar 2015. Koda yake kungiyar ta VW ta samu makudan kudi bayan sayar da dan wasan, amma za a yi kewar yadda De Bruyne ya taka leda a kungiyar ta 'Wolves'.
Lucas Hernandez - Euro Miliyan 80
Ya kasance dan wasa mafi tsada a tarihin FC Bayern Munich. A lokacin bazarar shekara ta 2019 Bayern ta sayi Lucas Hernandez a kan kudi Euro miliyan 80. A lokacin ya lashe kofin duniya da kasarsa Faransa a shekara ta 2018, Bayern Munich ta sayo shi daga kungiyar Atletico Madrid. Ya kasance dan wasa mafi tsada da aka saya a Bundesliga, kana dan wasan baya mafi tsada a duniya.
Jadon Sancho - Euro MIliyan 85
Daga Bundesliga zuwa Premier League: Bayan cimma yarjejeniyar Euro Miliyan 85, dan wasan dan asalin kasar Ingila mai shekaru 21 a duniya a wancan lokaci ya sauya sheka daga kungiyar Borussia Dortmund ta Jamus zuwa Manchester United ta Inglia a bazarar 2021. Ciniki mai kyau ga BVB, shekaru hudu bayan da ta sayi dan wasan a kan kudi Euro Miliyan bakwai da dubu 500 daga kungiyar Manchester City.
Josko Gvardiol - Euro Miliyan 91 da dubu 500
Ya kasance dan wasa baya na tsakiya, sai dai kwallon da ya ci ya sanya dan wasan kasar Kuroshiya ya dauki hankalin Pep Guardiola. Gvardiol ya ci kwallo a gasar zakarun Turai a watan Fabarirun 2023 ga kungiyarsa ta RB Leipzig a fafatawarsu da Manchester City da Guardiola ke horaswa. Watanni shida bayan kammala gasar, kungiyar ta Ingila ta saye shi ya zama dan wasan baya mafi tsada a duniya.
Randal Kolo Muani - Euro Miliyan 95
Ana dab da rufe hada-hadar cinikin 'yan wasa Bafaranshen ya bar kungiyarsa ta Eintracht Frankfurt a 2023. Ya kasance dan wasan da ya fi cin kwallaye a kakar Bundesliga, inda ya ci kwallaye 15 ya uma taimaka an ci 16. Duk da sayen sa a kan kudi Euro miliyan 95, kungiyarsa ta Frankfurt ba ta yi wani farin ciki ba. An saye shi jim kadan bayan rufe cinikin 'yan wasa a Jamus, babu damar yin ciniki.
Harry Kane - Euro miliyan 95
Bayan dogon cinki, maciyin kwallo a gasar Premier League ya koma FC Bayern, bayan kwashe tsawon lokacin kwallonsa a kungiyar Tottenham Hotspur. Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Ingila, ya kasance dan wasa mafi tsada da aka saya a tsawon sama da shekaru 60 na tarihin Bundesliga a kan kudi Euro miliyan 95.
Kai Havertz - Euro Miliyan 100
Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta yi cinikin dan wasan nan take a kan kudi Euro miliyan 80, a 2020. An sayi dan wasan mai shekaru 21 a wancan lokaci Kai Havertz daga Bayer 04 Leverkusen ta Jamus. Cinikin ya kai Euro Miliyan 100, ta la'akari da abin da ke da alaka da kwazonsa. Kwalliya ta biya kudin sabulu, domin a 2021 dan wasan dan kasar Jamus ya jagorance su lashe kofin zakarun Turai.
Jude Bellingham - Euro Miliyan 113
Bayan kwashe shekaru uku a Borussia Dortmund, dan kasar Ingilan ya koma Real Madrid a 2023 tare da saka hannu kan kwantirage zuwa 2029. Kudin cinikin da aka biya wani bangarensa ga kungiyarsa ta Birmingham City FC, zai karu daga baya ta hanyar garabasa zuwa Euro miliyan 113 kamar yadda kasuwar cininkin 'yan wasa ta 'transfermarkt.de' ta sanar.
Ousmane Dembélé - Euro Miliyan 135
A 2017 FC Barcelona ta sanya Euro miliyan 105 a asusun Borussia Dortmund, domin sayen Ousmane Dembélé. Kudin sun karu zuwa Euro miliyan 135 million, sakamakon garabasa da ya samu. Tun asali Dembélé da bai kasance dan wasa mai dadin sha'ani ga an saye shi ne a kan kudi Euro miliyan 14. A watan Disamba na 2023, Dembélé ya koma kungiyar Paris St. Germain tare da lashe kofin zakarun Turai a 2025.
Florian Wirtz - Euro Miliyan 150
A cinkin da ya kafa tarihi na kudi Euro miliyan 150, guda cikin kwararrun 'yan wasan Jamus ya sauya sheka. Maimakon ya koma FC Bayern da kila za ta so ta saye shi saboda kwarewarsa wajen iya sarrafa kwallo, Wirtz ya zabi ya koma kungiyar FC Liverpool ta Ingila. An dai saye shi a kan kudi Euro miliyan 125, inda za a rinka biyansa albashin Euro miliyan 12 zuwa 15 a shekara.