Najeriya za ta saye makaman yaki daga Amurka
August 14, 2025Amurkan dai ta sahalewa Najeriyar sayen wadannan makamai ne daga gare ta, bayan daukar lokaci Amurkan na bibiyar salon da Najeriyar ke bi a aikin tunkarar dimbin matsalolin tsaro da ke addabar ta.
Makaman dai da darajar su ta kai ta Dalar Amurka 346,da kuma suka hada da manyan bama-bamai masu cin dogon zangon IB 500, da Rokoki da ba sa kauce inda aka hara da su.
Za a saye su ne don tunkarar matsalolin tsaron kasar da suka ki ci, suka ki cinyewa, kama daga 'yan ta'adda da barayin daji masu kashe-kashen mutane tare da sace su don karbar kudaden Fansa da suka yawaita a arewacin kasar, sai kuma 'yan ta'addar rajin Biafra na IPOB a kudu maso gabas , da ma wasu sassan kasar da ake fama da rashin tsaro.
Garba Baba Umar ,tsohon Kwamishinan 'yan sanda,kuma tsohon shugaban sashen 'yan sandan kasa da kasa na Najeriya, wato Interpol, da kuma ya taba aikin bai wa shugaban Najeriya shawara kan dabarun dakile ta'addanci, na da ta cewa kan gabar da ake.
''Ba mi da isassun makamai, dan haka in har gwamnatin tarayya ta ce za ta kawo mana makamai, to wannan abin farin ciki ne. Wasu 'yan ta'addar ma za ka ga suna shigowa ne cikin kasarmu daga kasashen ketare,''
Wadannan makaman dai, an tabbatar cewar za su taimaka wa Najeriyar wajen aikin tunkarar matsalolin tsaro na yanzu da ma na nan gaba, wajen dakile gungun 'yan safarar mutane na kasa da kasa da gararin rashin tsaro da ke addabar zirin gabar Tekun Guinea.
Yankin a rewa maso gabashin Najeriya dai na kan gaba wajen fuskantar tsananin rashin tsaro a kasar, ga kuma dan yankin, a cewar Almustafa Jadadi :
''Wace irin barna ce ba a yi musu ba, an raba uwa da danta , an raba miji da matansa da yayansa,an raba 'yan uwa da 'yan uwa, ta yadda in aka ce ka nemo su ,ba ka san inda za ka nemo su ba.''
A shekarar ta 2022 dai, Amurkan ta sayar wa da Najeriyar kayayyakin yaki na Dala 997,da suka hada da kananan jirage 12 na kai hare-hare,da nau'rorin juyar da hari kan inda aka hara na zamani guda 2000,da kuma wadanda za su taimaka kai hari ko da da daddare ne.