Bill Gates zai tallafa wa Afirka da kudade masu yawa
June 5, 2025A Lagos ne cibiyar kasuwanci Najeriya aka gudanar da wani taro na yada nahiyar Afirka za ta kasance a sahun gaba cikin kasasshen da suka cigaba ta fannin kimiyya da fasaha da za ta samu tallafin Bill Gates
Taron da akai masa lakabi da gaba dai gaba dai Afirka ya sami halartar Bill Gates wanda yana daya daga cikin masu kudi na duniya da kuma Aliko Dangote wanda ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka.
Shi wannan taro kuwa an gudanar da shi ne bisa laimar gidauniyar Bill Gates Foundation inda a shekarun baya kadai kungiyar ta kashe sama da dalar Amurka miliyan dubu dari ga nahiyar ta Afirka inda kuma a yanzu ya ware akalla dalar Amurka kusan miliyan dubu dari biyu cikin shekaru 25 masu zuwa.
Bill Gates dai ya ce matukar ana son cigaba a nahiyar Afirka sai an bude kofar sanya hannayen jari domin samar da aikin yi ga jama'a tare kuma da hangen nesa.