Ci-gaban martanin jama'a a Nijar bayan cafke wasu sojoji
July 27, 2011Talla
A jamhuriyar Nijer wasu daga cikin iyallan sojojin ƙasar da hukumomin suka kama akan bisa zargin yunƙurin yin juyin mulki sun soma baiyana damuwar su dangane da halin da yan uwan na su suka shiga .Tare da yin kira ga gomnati da ta fito fili ta yi baiyani a game da dallilanta na ɗaukar wannan mataki. Har ya zuwa yanzu hukumomin ƙasar ta Nijar ba su tabbatar ko kuma ƙaryata wannan labari na kama sojojin ba .
Za a iya sauraron wannan rahoto daga ƙasa, sannan kuma za a ji hira da Abdourahamane Hassane ya yi da Nuhu Arzika ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyoyin farar' fula na ƙasar domin jin yadda suke tinkarar' lamarin.
Mawallafi : Gazali Abdu Tasawa
Edita : Abdourahamane Hassane.