Najeriya: Ci-gaba a yaki da cin-hanci
February 11, 2025Transparency International din ta ce a shekarar da ta gabata ta 2024, Najeriyar ta dan samu ci-gaba da maki daya a fanin yaki da cin-hanci. Rahoton na zuwa ne, a daidai lokacin da matsalar ta kara jefa milyoyin mutane cikin mawuyacin hali. Kungiyar ta Transparency International mai yaki da cin-hanci da rashawa a kasashen duniya, ta ce rahoton nata ya nuna cewa matsayin Najeriyar ya sauya a yakin da take da masu halin bera a cikin kasar musamman a tsakanin ma'aikatun gwamnati.
A yanzu Najeriyar na matsayi na 140, maimakon na 145 cikin kasashe 180 na duniya da aka yi nazari a kan matsalar cin-hanci da rashawa a cikinsu da take kai a baya. Akwai dai dalilai masu dimbin yawa da rahoton ya gano cewa sune suka sanya aka samu wannan ci-gaba a Najeriyar,duk da cewa rahoton ya ce binciken bai shafi cin-hanci da rashawa da ake zargin an tafka a kamfanonin masu zaman kansu da sauran 'yan kasuwa ba. Daya daga cikin kalubalen cin-hanci da rashawa shi ne yadda makudan kudi ke batan dabo a Najeriyar, abin da ke tayar da hankali.