China ta shirya inganta alaka da kasar Kanada
April 29, 2025China ta ce a shirye take da ta inganta dangantakarta da kasar Kanada, jim kadan bayna sanar da Firaminista Mark Carney a matsayin wanda ya lashe zabe a wani sabon wa'adi.
Sakamakon zaben na Kanada da aka yi a ranar Litinin, wata kyakkyawar alama ce ga jam'iyyar masu sassaucin ra'ayi, jam'iyyar da, da fari ta ga alamu na rashin katabus.
A shekarun baya dai dangantaka tsakanin China da Kanada ta yi tsami, musamman a lokacin da aka kama wani shugaban kamfanin fasahar sadarwar China a karshen 2018 a yankin Vancouver, da ma tsare wasu 'yan kasar Kanada da aka yi a China bayan an zarge su da leken asiri.
Haka nan ma kasar Kanada ta caccaki China a kan afkawa Hong Kong da ta yi a baya da ma matakanta a kan Musulmi 'yan kabilar Uyghur marasa rinjaye.